Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama A Dajin Zamfara

Rahotannin dake shigo mana da hukumar tsaro ta ?asa na bayyana cewar Jami’an tsaron ha?in guiwa sun hallaka yan bindiga a?alla 32 a dajin Zamfara wanda ya yi iyaka da jihar Neja, inda suka hallaka ‘yan Bindiga da dama wa?anda suka tsero daga Zamfara.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindigan suka kaiwa jami’an tsaro, inda suka harbe yan sanda 5 har Lahira, wa?anda suka yi kokarin maida martani.

Gumurzun ya faru ne a ?auyen Bangu Gari, dake ?aramar hukumar Rafi ta jihar Neja ranar Lahadi, kamar rahotanni suka tabbatar.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaro ya bayyana cewa wasu yan bindiga da suka fito daga Zamfara saboda ruwan wutan sojoji, sun fara kafa sansani a yankin.

“Adadi mai yawa na yan bindigan ?auke da muggan makamai, ciki harda roket, sun tattaru a yankin bayan tserowa daga sansaninsu dake Danjibga da Munhaye a ?aramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.”

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun farmaki caji ofi ?in yan sanda dake Bangu Gari, ?aramar hukumar Rafi, inda suka hallaka jami’ai 5.

“Nan take bayan samun rahoton faruwar haka jami’an tsaron ha?in guiwa suka nufi wurin domin kai ?auki.” “A ?arin karfi kuma sojoji sun yi wa yan ta’addan kwantan bauna yayin da suka yi kokarin tserewa ta hanyar garin Tegina.”

“A?alla mutum 32 sojojin suka kashe, cikinsu harda shugabanninsu, Karki Buzu da Yalo Nagoshi, yayin da wani babban ?asurgumin dan ta’addan, Ali Kawaji, ya samu muggan raunuka.”

Related posts

Leave a Comment