Da ?umi-?umi: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Mutum 18 A Kaduna

Wasu ?an bindiga sun kai hari Tashar Ka?anta a yankin Kutemeshi na ?aramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutum 19 a ranar Asabar.

Mazauna yankin sun ce ?an bindigar sun shigo ne misalin ?arfe 5 na yamma inda suka bu?e wuta suka abka shagunan mutane suka kwashi kayayyaki da suka ha?a da wayoyin salula.

Bayan kashe mutum 19, sun kuma raunata mutum 10, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.

Ya ce kuma yanzu da safiyar Lahadi ake shirin yi wa mamatan jana’iza.

?an bindiga masu fashi da satar mutane sun addabi yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka tarwatsa ?auyuka tare da tilastawa dubbai gudun hijira.

Related posts

Leave a Comment