?etare: Shugaban Kasar Chadi Zai Yi Tazarce Karo Na Shida

Jam’iyya mai mulki a Chadi ta amince shugaba Idriss Deby a matsayin ?an takararta inda zai nemi wa’adi na shida a za?en shugaban ?asar da za a yi a bana.

Deby mai shekara 68 ya shafe shekara 30 kan mulki a Chadi, kuma yanzu ana sa ran zai sake neman ?arin shekarun a za?en watan Afrilu.

Matakin ya haifar da zanga-zanga a ?asar, inda wakilin BBC a Ndjaména ya ce matasa da mata sun fito saman titi suna zanga-zanga domin adawa da takarar Deby da ke kan mulki tun 1990.

Jami’an tsaro kuma na ci gaba da farautar masu zanga-zanga kuma zuwa yanzu ba za a iya tantance yawan wa?anda aka kama ba ko suka ji rauni.

Duk da da?ewa kan mulki da kuma salon mulkinsa, amma Deby na samun goyon bayan ?asashen duniya musamman saboda tasirinsa ga ya?i da ta’addanci a yankin Sahel.

Mafiyawancin Shugabanni a kasashen Afirka ba sa mutunta tsarin yin zango biyu bisa karagar mulki kamar yadda tsarin dimukura?iyya ya shar’anta, suka yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin dacewa da bukatun su.

Related posts

Leave a Comment