Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana walwala a ?ananan hukumomi 21 dake Jihar, a yayin da sauran ?ananan hukumomi biyu Kaduna ta Kudu da Chikum zasu cigaba da zama cikin dokar kulle na awa 24 har abin da hali ya yi.
Bayanin hakan na ?unshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Kwamishinan tsaro na Jihar Samuel Aruwan ya fitar aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.
Aruwan ya bayyana cewar sauran ?ananan hukumomin Jihar zasu cigaba da zirga-zirga daga misalin karfe hu?u na asubah zuwa Shida na yamma.
Kwamishinan ya ?ara da cewar gwamnatin Jihar ta ?auki wannan mataki ne biyo bayan rahotannin da ta samu akan tsaro na cewar babu wata matsala ko barazana a yankunan kananan hukumomin Jihar 21.
Gwamnatin ta kuma bu?aci jama’ar ?ananan hukumomi biyu da dokar zata cigaba da aiki wato Kaduna ta Kudu da Chikum da su kasance masu bin doka da oda, ya zuwa lokacin da za’a janye dokar gaba ?aya.
Sannan sanarwar ta kuma bu?aci jama’ar jihar Kaduna da su cigaba da zama lafiya da juna da kai rahoton dukkanin wani da basu amince da take taken sa ga hukuma mafi kusa ko kuma a kira lambar wayoyi kamar haka 09034000060 ko kuma 08170189999.
