Da ?umi-?umi: Buhari Ya Bada Umarnin Bu?e Boda

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude iyakokin kasar nan guda 4. Ministar tattalin arzikin kasa da kasafin kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana hakan jim kadan bayan taron majalisar zartaswa da akayi ta kafar sadarwa.

Duk da an bude iyakokin kasar, hakan ba shi zai bada lasisin shigo da shinkafa da sauran kayayyakin da ake sarrafawa a kasar nan ba.

Idan ba a manta ba, gwamantin tarayya ta kulle iyakokin kasar nan fiye da kimanin shekara daya kenan yanzu inda ta bayyana dalilin rufe iyakokin kasar saboda bunkasa harkar noma,tattalin arziki da kuma kare yawaitar shigo da makamai cikin kasar ba ta hanyar da ta dace ba.

Batun rufe kan iyakokin Najeriya wani abu n da ya dade ana tattauna shi tsakanin jama’a, inda akasarin ‘yan Najeriya ke sukar matakin da gwamnati ta ?auka, yayin da wasu kuma suke goyon bayan gwamnati akan matakan rufe kan iyakokin.

Indai ba a manta ba gwamnatin Shugaban ?asa Buhari ta bayyana dalilan rufe bodar domin kariya da hana shigo da wasu haramtattun abubuwa cikin Najeriya, dangin makamai da miyagun kwayoyi.

Related posts

Leave a Comment