Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Dan takarar shugabancin Najeriya ?ar?ashin jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ?ir?iri batun sauya fasalin wasu takardun ku?in ?asar da batun ?arancin man fetur domin hana gudanar da za?en ?asar da ke tafe.
Bola Tinubu ya yi wa?annan kalamai ne a lokacin gangamin ya?in neman za?en shugaban ?asa na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Ogun ranar Laraba.
“Ba sa son za?en ya gudana. Suna bu?atar hana gudanar da shi. Shin za ku bar su?”, in ji Tinubu a lokacin da yake tambayar dubban magoya bayansa da suka halarci taron gangamin a filin wasa na MKO Abiola a birnin Abeokuta.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi kira ga ‘yan ?asar da su yi watsi da batun ?arancin mai, yana mai shawartarsu da su taka ?afarsu domin jefa ?uri’arsu a ranar za?en.
Ya ?ara da cewa za?en ?asar da ke tafe zai zama gagarumin sauyi ga ?asar.
“Sun fara zuwa da batun cewa ”babu mai”. Kada wannan ya dame ku, idan babu man fetur, za mu je da ?afarmu domin jefa ?uri’armu”.
“Idan kuna so ku ?ara farashin man fetur, ku ?oye man, ko ku sauya wa takardun ku?i kala, amma mu za mu ci za?e”, in ji Tinubu.
