Da Dumi-Dumi: Zan Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu – Sha’aban

?an takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a ?ar?ashin jam’iyyar APC Honorabul Muhammad Sani Sha’aban yace ko ka?an bai amince da hukuncin da Kotun daukaka kara dake Kaduna ta ya yi ba na cewar ba ta da hurumin saurarar karar da ya shigar dake ?alubalantar nasarar Uba Sani inda ta yi watsi da ?arar, inda ya sha alwashin ?aukaka ?ara.

Sha’aban ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da gidan Jaridar Muryar ‘Yanci ta wayar tarho, inda ya bayyana matakin da zai ?auka cikin gaggawa kan lamarin.

“Tuni na tattauna da lauyoyi na kan batun inda na basu umarnin sun shirya daukaka ?ara a ranar Litinin kan Kotun ta Kaduna na cewar ba ta da hurumin saurarar karar da aka shigar a gabanta da yin watsi da ?arar duk da tarin hujjoji da aka gabatar mata”.

Idan jama’a za su iya tunawa a hukuncin da kotun tarayya a garin Kaduna wanda maishari’a Mohammed Garba ya yanke, ya ce tun farko bai kamata akai maganar za?en fidda gwani kotu ba.

” Wannan Shari’a ba nan bane huruminta, rashin jituwa ce ta jam’iyya, domin ba akai ga za a ce wai kotu ta saka baki ba. Saboda haka wannan kotu ba za ta saurari wannan kara ba, ta yi watsi da shi.

Hakan ya tabbatar da takarar Uba cewa shine sahihin ?an takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

Related posts

Leave a Comment