Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘?an bindiga sun kashe Alhaji Rilwanu Gadagau wanda shi ne ?an majalisar jihar mai wakiltar Giwa Ta Yamma.
Wasu makusantansa sun shaida cewa maharan sun yi awon gaba da ?an majalisar ne tun a ranar Litinin da dare a lokacin da ?an bindiga suka kai hari a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Rahotanni sun ce an ga gawar ?an majalisar ne a cikin daji a safiyar Laraba.
A ranar Talata ne dai aka samu rahoton cewa ?an bindigar sun kai hari kan hanyar Kaduna zuwa Zaria inda aka tabbatar da mutuwar mutum ?aya da sace mutane da dama.
Sai dai mun tuntu?i rundunar yan sandan jihar Kaduna domin ?arin bayani ba su ?aga waya ba.
