Da Dumi-Dumi: Tambuwal Ya Haramta Aikin ‘Yan Banga A Sokoto

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta haramta ayyukan ?an sa-kai a fa?in jihar tare da ?arfafa aikin ?an banga.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da ?aukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ?ara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke ma?wabtaka da ita.

Ya ce suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da kyalewa ba domin mun san illar hakan.”

“Mun fito da doka da ta haramta ?an sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga,” in ji gwamna Tambuwal.

Sanarwar da ofishin gwamnan ta fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha ?aurin shekara 14 ko biyan tara ta naira 500,000.

Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha ?aurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.

Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta ?auki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar.

Kuma matakan hanyoyi ne na inganta sha’anin aikin ?an binga don taimakawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Related posts

Leave a Comment