Bakwai daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP sun yi murabus domin nuna adawarsu da abin da suke kira rashin tsarin shugabancin nagari.
Sai dai sun alkawarta ci gaba da yiwa jam’iyyar biyayya, amma sun ce ba za su ci gaba da shugabanci a kwamitin gudanawar na kasa ba.
An rawaito cewa mutanen da suka yi murabus sun hada da mataimakin sakataren kudi da mataimaki kan harkokin shari’a da akawu mai bincike kan harkokin jam’iyya, da mataimakin sakataren ya?a labarai, da shugabar mata da mataimakin sakataren shirye-shirye.
Mambobin sun zargi cewa akwai rashin tsari na shugabanci da kumbiya-kumbiya a harkokin shugabancin jam’iyyar.
