Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Amince A Cigaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun ?olin tarayya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin ku?in ?asar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ?asa ya bayar da umarnin sake fasalin ku?in da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.

Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.

Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ?olin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin ku?in ?asa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.

Related posts

Leave a Comment