Da Dumi-Dumi: Jirgin Shugaban Kasa Ya Nufi Landan

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin tarayya Abuja inda ya nufi birnin Landan na kasar Birtaniya a yau Lahadi.

Idan masu karatu sun tuna cewa a makon da ya gabata an shirya Shugaban kasan zai tafi Landan daga kasar Kenya bayan halartan taron majalisar dinkin duniya a Nairobi.

Rahotanni sun bayyana cewar shugaba Buhari zai ziyarci birnin na Landan ne domin duba lafiyar shi kamar yadda ya saba.

Related posts

Leave a Comment