Da Dumi-Dumi: Gogarman ‘Yan Ta’adda Turji Ya Tsere

Rahotanni da ga Jihar Zamfara sun baiyana cewa ?asurgumin ?an ta’addan nan, Bello Turji, wanda ya ke fashin daji da garkuwa da mutane a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya, ya tsere da ga sansanin da ya kafa sakamakon luguden wuta da ga dakarun Nijeriya.

A ?an kwanakin nan ne dai rundunar sojin Nijeriya ta tarwatsa sansanonin ?an ta’adda a hare-haren jiragen ya?i a Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyi sun baiyana cewa hare-haren jiragen ya?in ne ya tilastawa Turji da maya?an sa tserewa da ga dajin Fakai da ke ?aramar Hukumar Shinkafi zuwa kudancin Zamfara.

Majiyoyin sun ce an hango ?an ta’addan su ma kafa tantuna a dajin Gando da ke ?aramar Hukumar Bukkuyum.

Kusan ma dai yan ta’addan me ke ri?e da garin, inda ?an garin da abin ya rutsa da su ke cewa ?an rashin dajin sun kakkafafa bukkoki kuka a babura su ke tafiya, yayin da wasu kuma su ke tafiya a kafa tare da dabbobin da su ke ?wacewa al’umma.

Jaridar ta ?ara da cewa ba ta samu damar samun kakakin rundunar ?an sanda na Zamfara, SP Muhammad Shehuba yayin ha?a rahoton.

Related posts

Leave a Comment