Da Dumi-Dumi: Emefiele Ya Maka Gwamnatin Tinubu Kotu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Mista Godwin Emefiele ya shigar da ?ara a gaban wata babbar kotun tarayya, yana ?alubalantar tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke yi.

A cikin ?udurin da ya gabatar, Emefiele ya nemi kotu ta tilasta wa hukumomi tabbatar masa da ‘yancinsa na walwala da ‘yancin zirga-zirga, don kuwa a cewarsa, babu hujjar ci gaba da tsare shi.

Sai dai, Ofishin Atoni Janar na Tarayya da kuma hukumar DSS sun ce tsare dakataccen gwamnan bankin yana kan doka.

Sun kuma ce tsare jami’in ya dogara ne kan wani umarnin kotun majistare don haka suka nemi babbar kotun ta kori bu?atar da Emefiele ya gabatar.

Sun nunar da cewa kama tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya yana kan tsarin gudanarwa na hukumar ta DSS.

Yayin da Atoni Janar na Tarayya ya ?alubalanci hurumin kotun na sauraron ?arar, saboda ?udurin da Godwin Emefiele ya gabatar na neman kotu ta jingine umarnin tsare shi ne, maimakon neman a tabbatar masa da ‘yancinsa.

Haka zalika, ita ma hukumar DSS a nata ?angare ta ?alubalanci ?udurin neman beli da Mista Emefiele ya gabatar.

Daga bisani, kotu ta ?age shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Yuli don yin hukunci kan wannan bu?ata.

A ranar 10 ga watan Yuni ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga matsayin Gwamnan Babban Bankin ?asar, daga bisani kuma hukumar DSS ta sanar da cewa tana tsare da shi.

Related posts

Leave a Comment