Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ?addamar da sabon tsari kan rage yawan jama’a don ci gaba mai dorewa a Najeriya.
Shugaban ya ?addamar da wannan shiri ne a fadarsa da ke Abuja babban birnin ?asar.
Shugaban ya ce akwai bu?atar ?aukar matakan gaggawa domin shawo kan ?aruwar da ake samu na haihuwa ta hanyar fa?a?a shirye-shiryen samar da hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani a fa?in ?asar.
Domin tabbatar da wannan tsarin, shugaban ya kafa wani kwamiti da zai ri?a sa ido kan yawan jama’a wanda shi da kansa zai jagoranta, sai kuma mataimakinsa zai ci gaba da taimaka masa a wannan ?angare haka kuma akwai shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnatin a matsayin mambobi.
Shugaba Buhari ya ce babban burin wannan shiri shi ne inganta rayuwar duka yan Najeriya wanda hakan na daga cikin abin da gwamnatin ?asar ke son cimmawa.
Buhari ya ce ?an Najeriya sun fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afrika kuma ita ce ta bakwai a duniya baki ?aya kuma tana daga cikin ?asashe ?alilan na duniya da ake ?ara samun haihuwa sosai – ?asar ta dogara kan matasa inda sama da kashi 72 cikin 100 na matasan na ?asa da shekara 30 inda rabin matan ?asar na cikin shekarunsu na haihuwa wato tsakanin shekara 15 zuwa 49.
Ganin cewa kafin a ?addamar da wannan shiri akwai bu?atar samun sahihai da ingantattun bayanai kan adadin jama’a a Najeriya, Shugaba Buharin ya bayyana cewa bayanan da za a samu daga ?idayar da za a yi a 2022 za ta samar da duka bayanan da ake bu?ata domin aiwatar da shirin na tsarin iyali.
