Sufeton Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya nemi a dakatar da Abba Kyari daga aikin ?an sanda bisa zargin kar?ar cin hanci da ‘yan sandan Amurka ke yi masa.
Kazalika, IGP ?in ya kafa wani kwamati na mutum hu?u ?ar?ashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari mai mu?amin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).
Usman Alkali ya bayar da shawarar dakatarwar ce cikin wata wasi?a da ya rubuta wa Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ranar Asabar, yana mai cewa matakin “?aya ne daga cikin matakan ladaftarwa na rundunar ‘yan sanda”.
Ana zargin Abba Kyari da kar?ar rashawa a hannun matashi ?an Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa. Sai dai Kyari ya musanta zargin.
Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da ?ai?aikun mutane.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ?aukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.
