Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar an yi nasarar hallaka shahararren ?an ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Dogo Gide a wani gumurzu a dajin Kuyanbana.
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna. A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa Gide ya mutu ne a ranar Lahadi bayan mataimakin kungiyarsa na yan Bindiga, Sani Dan Makama ya bindige shi kamar yadda ya yi wa Buharin Daji.
Tsohon shugaban ‘yan bindigan ya dade yana adabar garuruwa a jihohin Zamfara, Niger, Kaduna, Katsina da Kebbi tsawon shekaru.
Majiyar ta ce: “Mataimakin Dogo Gide wanda ake kira Sani Dan Makama ne ya kashe shi bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a dajin Kuyambana da ya hada Zamfara – Birnin Gwari da Dogon Dawa.”
