Labarin dake shigo mana yanzu haka daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu ri?a?un ?an fashin daji biyu da suka addabi jihar da ma?wabtatanta da suka ha?ar da Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta.
Jaridar PrNigeria ta rawaito cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya a wasu dazuka da ke ?auyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji.
Kafin mutuwarsu dai suna cikin gawurtattun ?an fashin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya.
Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren.
