Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an sanar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki.
Bayanai daga farfajiyar filin taro na Eagle Square dake birnin tarayya inda ake gudanar da taron gangamin jam’iyyar APC na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama sabon shugaban uwar jam’iyyar.
Tuni Gwamnoni, Sanatoci, yan majalisa da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka taya Abdullahi Adamu murnar wannan nasara.
Nasarar ta shi ta biyo bayan janyewa da sauran ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar suka yi ne domin biyayya ga umarnin mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari.
Babban kalubale da sabon shugaban zai fuskanta sun hada da kokarin ha?a kawunan ‘yan jam’iyyar wa?anda rikicin cikin gida ya raba a mafi yawancin Jihohi.
