Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da fa?ada dokar hana walwala a ?auka cin jihar gaba ?aya na tsawon awanni 24, kuma dokar ta fara aiki nan take.
Hakan ya biyo bayan fargabar da ake da ita ne na ya?uwar tashin hankali a fa?in jihar mai jama’a daban-daban mabanbanta Addini.
An bai wa jami’an tsaro umarnin damke dukkanin wanda aka kama ya yi kunnen ?ashi da wannan doka ta hanyar karyata, ta hanyar diban kayayyakin jama’a da kokarin haddasa fitina, kuma jami’an tsaro zasu cigaba da sintiri har abin da hali ya yi.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi tir da abubuwan da ake ta ya?awa a kafafen sadarwa na zamani na yunkurin tayar da hankula gami da kwasar kayayyakin jama’a da wasu ke yi. Sannan an bukaci jama’a da zama ‘yan kasa nagari masu martaba doka da oda.
Bayanin hakan na ?auke cikin wata takardar sanarwa da Kwamishinan tsaro na jihar Mista Samuel Aruwan ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.
