Da ?umi-?umi: An Yi Wa Buhari Allurar Rigakafin CORONA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kar?i allurar rigakafin korona a ranar Asabar.

Likitan shugaban ne Dr Shu’aibu Rafindadi ya yi wa shugaban allurar misalin ?arfe 11:53 a fadarsa a Abuja.

An kuma yi wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo allurar bayan yi wa shugaba Buhari.

An kuma gabatar da katin shaidar kar?ar allurar ga shugaban da kuma mataimakinsa.

A jawabinsa bayan kar?ar allurar, shugaba Buhari ya yi kira ga ?n Najeriya su fito domin a yi masu allurar.

A ranar Juma’a ne Najeriya ta ?addamar da allurar rigakafin korona a ?asar inda aka fara yi wa likitoci kafin shugabanni da kuma sauran ?an ?asa.

Allurar riga-kafin Oxford ta AstraZeneca Najeriya za ta kar?a a ranar Talatar makon da ya gabata.

Najeriya za ta kasance kasa ta uku a yankin Afrika Ta Yamma da suka ci moriya tallafin alluran riga-kafin karkashin shirin COVAX, baya ga Ghana da Cote D’Ivoire.

Related posts

Leave a Comment