CORONA: An Kulle Jihar Ekiti

Gwamnatin jihar Ekiti ta saka dokar hana fita a fadin jihar Ekiti inda dokar za ta fara aiki daga yau Litinin, 11 ga watan Janairun 2021.

Dokar za ta rin?a aiki ne daga 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Gwamnatin jihar dai ta saka wannan doka ne a yun?urinta na da?ile ya?uwar annobar korona. Hakan ya sa gwamnatin ta kuma hana taruwar mutum sama da 20 a wuri guda har sai abin da hali ya yi.

Kwamishinan ya?a labarai na jihar, Akinbowale Omole ya bayyana cewa gwamnati na son ?aukar matakan da?ile cutar domin kare mutanen jihar.

Saka wannan doka na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar da ke da?ile cutuka masu ya?uwa NCDC ta sanar da cewa wa?anda suka kamu da korona a Najeriya sun zarce 100,000.

Related posts

Leave a Comment