Sa-toka-sa-katsi da sa-in-sa sun ?arke tsakanin Najeriya da Amurka, a ?o?arin da Najeriya ke yi na ganin ta kar?o ku?in ta har Dala miliyan 8.6, wa?anda gwamnatin Amurka ta ?wace tun cikin 2015.
Tun bayan ?wace ku?a?en dai Amurka ta ?i sakin ku?in bisa dalilan cewa an nemi a sayi makaman ba bisa ?a’idar da doka ta gindaya ba.
Tun da farko dai Najeriya ta biya ku?in ta hannun wani kamfanin dillacin makamai na Amurka, mai suna Dolarian Capital Inc (DCL), cikin 2014, domin sayo makamai a Amurka, bayan ‘yan Boko Haram sun sace ?aliban Chibok su 276, a Jihar Barno.
Sai dai kuma an samu tangar?a yayin da Gwamnatin Amurka ta ?i rattaba wa DCI hannun amincewa ya yi wa Najeriya dillacin makaman da kuma aika su Najeriya.
Nan da nan sai Gwamnatin Amurka ta garzaya kotu, inda kotu ta bada sammacin ?wace ku?a?en, bisa dalilan cewa cinikin ya karya dokar Cinikin Makamai Tsakanin Amurka da ?asashe.
