Cin Zarafin ?an Adam: Yarima Zai Gurfana Gaban Kwamitin Bincike

Kwamitin bincike mai zaman kansa watau IIP da hukumar NHRC ta kasa ta kafa, ya bukaci Ahmad Sani Yeriman-Bakura ya bayyana gabansa, domin amsa wasu tambayoyi game da zargin cin zarafi da ake yi mishi.

A ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, 2020, hukumar ta fitar da rahoton ta na mai bayyana cewar kwamitin na neman tsohon gwamnan ruwa a Jallo.

Kwamiti ya umarci Sanata Ahmad Sani Yeriman-Bakura ya hallara a ranar 12 ga watan Janairu, 2021, kamar yadda rahoton ya bayyana.

An aika wa tsohon gwamnan na jihar Zamfara wannan sammaci ne bisa zarginsa da ake yi da amfani da jami’an ‘yan sanda wajen cin zarafin wani bawan Allah mai suna Alhaji Musa Wapa ta hannun jami’an tsaro.

Ana zargin fitaccen ‘dan siyasar da tsare Musa Wapa, wanda attajirin ‘dan kasuwa ne, inda aka rika galabaitar da shi bayan an cafke shi.

Alhaji Musa Wapa babban ‘dan kasuwa ne wanda ya samu sabanin kudi har Naira miliyan 23 tsakaninsa da Sanata Ahmad Sani Yeriman-Bakura.

Wanda yake jagorantar wannan kwamitin bincike da hukumar kare hakkin Bil Adama ta Najeriya ta kafa shi ne tsohon Alkali Suleiman Galadima.

Suleiman Galadima ya bayyana cewa wanda ya kawo karar ya yawaita ambatar sunan ‘dan siyasar, wanda hakan ya sa aka bukaci ya gabatar da kansa.

Related posts

Leave a Comment