Tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima ya ce bai yi niyyar cin zarafi ko muzanta kowanne dan takara ba, ballatana abokaina da abokan shawarata a kalaman da na yi.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channel ya yi dashi a Abuja.
“Duk cikinsu babu dan hamayya don haka bukatarsu ta tsayawa takara ba barazana ba ce a gare mu,” in ji tsohon gwamnan na Jihar Borno.
Sanata Shettima ya kara da cewa an zuzuta kalaman da ya yi a kan Osinbajo da Ahmad Lawan kuma ba a fahimce su ba.
Ya kara da cewa “duk da haka ina neman afuwa ga mataimakin shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa bisa radadin da wadannan kalamai nawa suka yi musu.
