Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada tsohon shugaban hafsin sojan kasa Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin.
Kazalika shugaban ya nada tsohon babban hafsan tsaron kasar Janar Abayomi Gabriel Olonisakin mai ritaya a matsayin jakadan Kamaru.
An gabatar musu da wasikun kama aikin ne yayin wani ?an kwarya kwaryar biki da ministan harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama ya jagoranta ranar Talata a Abuja
