Buhari Ya Yi Kuka Sakamakon Rasuwar Bashir Tofa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin hawaye ya mi?a ta’aziyyar rasuwar tsohon ?an takarar shugabancin ?asar Bashir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin “cikakken ?an kishin ?asa”.

“Ha zuwa lokacin rasuwarsa, cikakken ?an kishin ?asa ne. Ya nemi kafa ingantacciyar Najeriya ga kowa da kowa,” a cewar Buhari cikin sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.

Sanarwar ta ?ara da cewa Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya ji ?an sa sannan ya bai wa iyalai da abokansa ha?urin rashinsa. “Muna addu’ar a?idarsa ba za ta gushe tare da shi ba,” in ji Buhari.

Kazalika, Buhari ya tura tawagar ta’aziyya zuwa Jihar Kano da ta ?unshi jami’an gwamnati da suka ha?a da ministan tsaro, ministan harkokin ruwa, babban akanta na ?asa, da kuma Garba Shehu kakakin fadar shugaban ?asa.

Bashir Othman Tofa ya rasu da asubahin Litinin yana da shekara 74 bayan ya sha fama da jinya kuma an yi jana’izarsa a birnin Kano.

Related posts

Leave a Comment