Buhari Ya Yi Kiran Gamawa Da ‘Yan Bindiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin ?asar su yi amfani da ?arfi wajen mur?ushe ?an bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja da ke tsakiyar ?asar.

Cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce shugaban ya bayar da umarnin ne ga shalkatar ta Najriya.

”A matsayinsa na babban kwamandan sojojin Najeriya, shugaban ?asa ya shirya wani gagarumin farmakin soji a jihar Neja wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ?an Boko Haram da ke tserewa aga arewa maso yamma, da kuma arewa maso gabashin ?asar nan” in ji sanarwar.

A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja kuwa shugaban ya ce “Ina so in mi?a sa?on ta’aziyya gareku, sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan”.

Ya ci gaba da cewa “A shirye gwamnatin tarayya take ta ?arfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ?an kasa, tabbas za mu shawo kan wannan matsala,” in ji shugaban kasar.

Related posts

Leave a Comment