Rahotanni dake shigo mana daga birnin Santanbul na ?asar Turkiyya na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanka kek ?in murnar ranar haihuwarsa a Turkiyya bayan ya cika shekara 79 da haihuwa.
An tsara kek ?in da launin Najeriya wato fari da tsanwa inda bayan ya yanka kek ?in sai ya tattauna da hadimansa kafin suka tafi wajen taron tattaunawa kan cinikayya tsakanin Turkiyya da ?asashen Afrika.
Shugaban ?asar ya bayyana cewa zai ci gaba da yin iya bakin ?o?arinsa wajen yi wa ?an Najeriya aiki har zuwa lokacin da zai mi?a mulki a 2023.
Shugaban ya kuma ce zai koma gona ne domin ci gaba noma da kiwo bayan ya mi?a mulki.
