Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya taya takwaransa na Senegal Macky Sall murna, bayan da kasarsa ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika.
Tawagar Teranga Lions ce ta yi nasarar lashe kofin na gasar AFCON da aka kammala a Kamaru makon da ya wuce.
Shugaba Buhari ya yi murnar ne yayin da yake karbar bakuncin jakadan Senegal a Najeriya Babacar Matar Ndiaye a fadarsa da ke Abuja
