Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar Imo ta yamma Rochas Okorocha ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya yi alkawarin bibiyar binciken da hukumar EFCC ta ke yi masa.
Rochas Okorocha ya yi wannan bayani ne da yake zantawa da manema labarai jim ka?an bayan haduwarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce hukumar EFCC na cigaba da matsa masa lamba duk da cewa kotu ta bada umarni a daina binciken da ake yi.
Sanata Okorocha ya ?ara da cewa ya zauna da Mai girma shugaban kasa ne da nufin a san yadda za ayi EFCC tayi masa adalci domin an karbe masa fasfo. A cewar ‘dan siyasar, nauyin shugaban kasa Buhari ne ya tabbatar an yi wa ‘yan kasa adalci.
“Shugaban kasa ya ce zai bibiyi lamarina zuwa gaba, musamman da ya ga hukuncin da kotu tayi. Ya ce zai bibiya ya ga asalin abin da yake faruwa.” “Ina kuma fata zai yi hakan, na yi imanin cewa zai yi wannan.”
Da aka tambaye shi a game da silar bincikensa da hukumar ta EFCC ta ke yi, ‘Dan majalisar dattawan ya ce akwai siyasa a lamarin saboda takararsa.
“Na zo nan ne domin in nemi a yi mani adalci a matsayinsa na shugaban Najeriya. Ya kamata ya san abin da yake faruwa. Ban ce ka da a bincike ni ba.”
