Borno- Zulum Zai Sake Gina Garin Malam-Fatori

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnatin jihar Babagana Umara Zulum na shirin sake gina garin Malam-Fatori wanda jama’ar garin suka bar shi wurin shekaru bakwai da suka gabata bayan harin ‘yan ta’addan Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewar da yawa daga cikin mazauna garin sun garzaya Bosso da Diffa ta jamhuriyar Nijar domin neman mafaka tun a shekarar 2014.

Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a ya ziyarci garin Malam-Fatori, hedkwatar karamar hukumar Abadam wacce ke yankin tafkin Chadi na arewacin Borno.

A wata takarda da mai bada shawara ga gwamnan na musamman, Malam Isa Gusau ya fitar a Facebook, ya ce sun kai ziyarar ne domin fara duba yadda za a gyara wurin kuma ‘yan gudun hijira su dawo daga Bosso da Diffa a jamhuriyar Nijar.

Zulum ya amince da bada motocin sintiri 10 domin inganta tsaro kuma ya tattauna da babban kwamandan bataliya ta 68 dake Malam-Fatori domin gano wuraren da gwamnatin jihar Borno za ta bada tallafi.

A yayin jawabi ga dakarun, Zulum ya jinjinawa kokarin dakarun tare da basu kwarin guiwa kan su cigaba da kokari wurin kawar da ragowar ‘yan ta’adda dake kusa da Malam-Fatori.

Gwamnan daga bisani ya duba abubuwan more rayuwa da ‘yan ta’addan suka lalata a garin wanda yace za a gyara su kafin watan Disamba.

Related posts

Leave a Comment