Borno: APC Ta Kafa Kwamitin Sasanci

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta kafa wani kwamiti domin sasanta ?a?an jam’iyyar da ke da ?orafe-?orafe bayan za?ukan fitar da gwanin da aka gudanar a fa?in jihar.

Shugaban jam’iyyar na APC a Jihar Borno Ali Bukar Dalori ne ya ?addamar da kwamitin a Maiduguri.

Ya bukaci kwamitin ya ziyarci dukkan ?an jam’iyyar da suka nemi yin takara a mukamai daban-daban amma ba su gamsu da sakamako zabukan ba.

Baya ga lauya M.T. Monguno da Adamu, akwai kuma Mohammed Makinta, Alhaji Kaumi Damboa, Babagana Malarima, Sani Kuli Askira, Modu Kawu Ngamdu, Babagana Tijjani Banki da kuma Zakari Dali Bayo cikin mambobin kwamitin.

Related posts

Leave a Comment