Borno: An Yi Nasarar Cafke Dillalan Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Hukumar Sojin Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin dan Boko Haram a Arewa maso gabas kuma ta kai simame ma’ajiyar sinadaran hada bama-bamai a jihohin Borno da Yobe.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabin da ya saki a shafin Facebook.

Yace wannan nasara ya biyo bayan hare-haren da rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) suka kai. Yace: “Dakarun Sector 2 Joint Task Force na Operation HADIN KAI (OPHK) sun damke wani babban dan Boko Haram kuma sun kai simame ma’ajiyar ajiyan sinadaran hada bama-bamai a Damboa dake jihar Borno; da kuma Gashua dake jihar Yobe.”

“Sakamakon cinne, an damke wani dan ta’addan BH/ISWAP da aka dade ana nema ruwa a jallo a hanyar Damboa-Wajiroko.”

Ya kara da cewa Sojoji sun kwato buhuhunan sinadarin Urea 281 a ma’ajiyoyi daban-daban kuma an damke masu kaiwa Boko Haram wadannan kayayyaki mutum biyu.

“Hakazalika, Sojoji sun samu nasarar damke wasu masu kaiwa yan ta’adda sinadaran hada bama-bamai. Kasuwar ta shahara da taya yan Boko Haram boye sinadaren.”

“A harin da aka kai, an damke buhuhunan Urea 281 daga kasuwar kuma an damke masu sayarwa Boko Haram.”

Related posts

Leave a Comment