Biredi Ya Yi Tashin Gwauron Zabo A Najeriya

Kungiyar masu burodi ta umarci duka mambobinta da su ?ara farashin kayansu da kashi 30 cikin 100 saboda ?aruwar farashin sinadaren ha?a burodin da dangoginsa.

Umarnin na zuwa ne ranar Alhamis bayan da aka cimma matsayar a ?arshen tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar da aka yi a Abuja.

Da yake bayani kan dalilan ?ara farashin, shugaban ?ungiyar na kasa Mansur Umar ya ce ?aruwar farashin siga da bota da fulawa duka na cikin abubuwan da suka janyo ?aukar matakin.

Shugaban ya ce farashin fulawar da suke saya a ?asa da naira miliyan shida a duk mota guda, yanzu suna sayanta kan miliyan tara.

Nawa ne ?arin da aka yi?

Cikin tattaunawarsa da BBC Hausa, mai magana da yawun ?ungiyar masu burodi, Kabiru Hasssan Abdullahi, ya ce an ?ara farashin ne da kashi 30 cikin 100.

“Kusan dukkan jihohi sun fara aiki da sabon farashin amma mu a Kano yau (Laraba) muka dawo, za mu kira taron masu gidan burodin,” in ji shi.

Hakan na nufin burodin da ake sayarwa N100 zai koma N130. Na N200 zai koma N260, yayin da na N400 zai zama N520.

“Mu kanmu muna cikin matsala, idan ka duba gidajen burodin da aka rufe daga shekara ?aya zuwa yanzu suna da yawa,” in ji Kabiru Hassan.

“Mun yi iya ‘yan dabarunmu don kar a ?ara amma babu yadda za mu yi, in ana son burodin ya fita da inganci dole ya fita da nauyinsa, shi ne zai zama lafiyayyen abinci.”

Ya ?ara da cewa an samiu ?arin naira 3,000 a kan kowane buhun fulawa cikin shekara ?aya, wanda ya kai kusan kashi 50 cikin 100.

Related posts

Leave a Comment