Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Sace ?an Majalisa

Wasu ‘yan bindiga sun sace tsohoon ‘dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdulmumuni Ningi.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sace tsohon dan majalisar, wanda ya taba wakiltar mazabar Ningi a majalisar jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar ta Bauchi, Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka, inda yace an yi garkuwa da tsohon dan majalisar a cikin garin Bauchi.

Sha’anin satar mutane da yin garkuwa da su wani abu ne wanda ya zama ruwan dare yanzu a Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar, inda ‘yan Bindiga da barayin shanu ke cin karensu babu babbaka.

Babbar hujjar da ake sukar Gwamnatin Buhari da ita shine hauhawar samuwar masu garkuwa da mutane a karkashin gwamnatin shi wanda kaso dari bisa ?ari Fulani ne, kisan jama’a da tatsar ku?a?e a hannun su ya zama ba a bakin komai ba a wajen su.

Related posts

Leave a Comment