Bauchi Ministar Jin ?ai Ta Raba Ku?i Dubu 20-20 Ga Matan Karkara

Bauchi: Ministan Jinkai ta Raba Kudi 20,000 ga Matan Karkara a Azare.Ministan ma’aikatar Jinkai, da ci gaban al’umma Sadiya Umar Farouk ta raba kudi ga mata, kyauta domin ci gaba da harkokin sana’o’in su, tare da dogaro da kai, su kimanin 54,738, a fadin jihar wanda aka fara da kananan hukumomin jihar tara 9 a yankin Azare, wanda suka hada da karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

Yayin da take kaddamar da shirin rabon kudin a wajen taron, tace gwamnatin tarayya tayi wan nan shiri ne don rage radadin talauci a Najeriya,

Sadiya Farouk, wadda mataimakin tsare-tsare na ma’aikatar Dr.Abubakar Sulaiman ya wakilce ta a wajen taron, ta kara da cewa wadanda zasu ci gajiyan kudin mafi yawancinsu matan karkara ne wanda ake sa ran kimanin su dubu dari da hamsin 150,000 zasu karbi naira dubu ashirin 20,000 a dukkan fadin Najeriya.

Sadiya Farouq tace tuni rabon kudin yayi nisa a sauran jihohin kasan, inda gwamnatin take da aniyar cire talauci ga mutum miliyan 100 yan Najeriya a sheka ta 2030.

Tace “naira dubu ashirin zai tallafa ma matan ta wajen bunkasa tattalin arzikinsu, dama arzikin kasa baki daya”. tare da basu shawara kan yin amfani da kudin ta fannonin saye da sayarwa, ba abi dasu ta wata hanya ba.

Kana ministan ta yabawa gwamnan Jihar Bala Mohammed ta wajen hangen nesa, kan samar da hanyoyin ci gaba a jihar, tace nan bada dadewa ba matan zasu fita daga kangin talauci.

Yayin da yake jawabin bude taron mai martaba Sarkin Katagum wanda Makaman Katagum. Aliyu Hussaini ya wakilce shi, ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya, cewa babu shakka kudin zai kawarda talauci a cikin al’umma.

Daya daga cikin wadanda suka ji gajiyar tallafin kuwa, Hauwa Mohammed tace “kudin da aka bani zanyi amfani dashi wajen sarin kayan gwanjo na yara, ina sayarwa”.

“Zai taimakamin wajen tuyan kosai da nake yi, dama jarin bashi nake yi bai taka kara ya karya ba, amma yanzu dubu ashirin, sai godiya ma Baba Buhari da Minista Sadiya Farouq, mungode sosai”. Inji Hajara Mohammed.
#

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment