Bauchi: Matasan APC Sun Jinjina Wa Shugaban Majalisar Dattawa

Daga Adamu Shehu Bauchi

Ha?akar Kungiyar matasan APC na Arewa maso gabas da aka fi sani da suna (APC Coalition Network) sun fito sun jinjina wa Shugaban Majalisar Dattawa, Alhaji Ahmed Lawal kan irin ayyukan da yake wa mazabarsa da kuma kasa baki daya

Sannan sun bayyan goyon bayan su ga Ahmed Lawal da irin gudummuwar da yake bada wa a Shugabancin majalisa suka ce shi shugaba ne na gari don haka a koda yaushe suna nan tare dashi

Shugaban Kungiyar reshen jihar Bauchi Adamu Zailani shine yayi wannan yabo a madadin sauran ‘ya’yan Kungiyar a wani taro da suka shirya a garin Bauchi.

Ya ?ara da cewa irin namijin kokarin da Ahmed Lawal yake yi a fagen shugabanci a cewarsa ya jima yana taimako ta fannoni da dama a rayuwar mutane.

Zailani yace kungiyar an kirkiro ta ne domin Samar da hadin kan ‘ya’yan Jam’iyyar APC na yankin arewa maso gabas don jawo hankalin ‘ya’yan APC da basu hakuri kan abubuwan dake faruwa na siyasa a ciki Jam’iyyar

Bugu da ?ari, yace kungiyar tana da shugabanci da madafun iko a dukkan kananan hukumomi 774 na Najeriya da shugabanni a matakai da dama

Har-ila yau, yace hadakar Kungiyar za ta tantance ‘yan takarar Jam’iyyar APC a yankin su saboda gudun komawa gidan jiya, sai an fara tafiya sai kaji kwatsam an dakatar da ?an takara bayan yayi ?are-?are akan kijerar.

Daga karshe Shugaban Kungiyar yace tun bayan dawowar mulkin damokradiya a shekara 1999 yake yi wa al’umma hidima tun ma kafin ya shiga majalisar Dattawa, gashi kuma a halin yanzu shine na Uku a Najeriya a tsarin mulkin kasar.

Related posts

Leave a Comment