Bauchi: Mata Na Bada Gudunmuwa Wajen Shugabanci Nagari – Uwargidan Gwamna

Uwar gidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Mohammed ta bayyana cewa mata suna taka muhimmiyar rawa da ginshikin samar da shugabanci na gari, idan akayi la-akari da hidimar tarbiyan al’umma.

Ta fadi hakan ne a wajen wata bita na kwana biyu 2 da offishinta ya shirya ma matan kwamishinoni da matan shugabbanin kana nan hukomomi, tare da hadin gwiwan wata kungiya mai zaman kanta (Synistania Nig Limited) wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnati

Aisha Bala ta jaddada cewa matan shuwaganni a matakai dabam-dabam suna da jan aiki ta wajen fadakarwa da nusar damn al’umma musamman matasa kan shugabancin da ake masu, na gari ko akasin hakan.

Bugu da kari ta kirayi mata da su ci gaba da aiwatar da ayyukansu na jinkai da tausayawa, kana tace sunyi amfani da abubuwan da aka gaya masu a yayin bitar, in sun koma cikin al’ummar da suke shugabanta, hakan zai bama gwamnati samun nasara a gudanar da shugabancin mutane.

“Ina mai maku gargadi da zaman lafiya da kowa, a duk inda kuka samu kanku, tace babu al’ummar da zata ci gaba cikin rudani da tashin, hankali, zaman lafiya yafi komai”. Ta fada.

Anashi jawabin maraba, kwamishinan kana nan hukomomi da masarautun gargajiya Alhaji Abdurrazak Nuhu Zaki, ya yabawa uwar gidan gwamnan kan irin aiyukkan ta na jinkai da kuma shirya irin wan nan taro na karin ilimi.

Yace “Kina cire ma mata kitse a wuta ta wajen wayar masu da kai, ina jan hakalin wadanda aka shirya taron domin su, da suyi amfani da damar da suka samu, kar su rika dinki ana warwarewa, yace su rika koyi da irin ayyukan da Uwar gidan gwamnan take yi, da kuma dogaro da kai, don tabbatar da shugabanci na gari”.

Har ila yau, shugaban hukumar kula da marasa galihu da kana nan yara ta jihar Bauchi, Mrs. Hassana Arkila tace wan nan bitar yazo a daidai, kuma tace sai an hada karfi da karfe kafin a samu nasarar abunda gwamnati tasa gaba akai, ta kara da cewa dole ne a sake sabon lale ta wajen tarbiyyar yaran mu, musamman a arewacin Najeriya.

“Baza musa ido yaranmu suna lalacewa ba, da shaye shaye da sara suka, da fyade da fashi da makami, dukkan mu muna da aiki tukuru a gabanmu kan tarbiyyar yayan mu baki daya”.

A wajen taron daya daga cikin kasidar da Dr. Musa Adamu Wunti, na Jami’ar Jihar Bauchi dake Gadau, ya gabatar da takarda inda tayi nuni da cewa “mata suna da kaso mai tsoka ta wajen gina al’umma, da kuma shuganci na gari, bin doka da oda da zimman ayyukan da zasu kawo ci gaba, da zaman lafiyan jama’a baki daya”.
#

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment