Daga Adamu Shehu Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta kaddamar da shirin tallafin rage radadin talauci na ki manin naira miliyan dari ga mutane dubu daya 1000 a kananan hukumomin Itas/Gadau da Jama’are. Wanda gwamna Bala Mohammed ya kaddamar a ranar Lahadi a cikin Shirin da akayi mai lakabi da (Cika Alkawari).
Gwamna Bala a wajen taron yace Kawar da Talauchi shine abunda gwamnatin sa tasa a gaba don halin da aka shiga na koma bayan tattalin arzikin kasa a Bauchi da ma Najeriya baki daya.
Ya kara da cewa mutane suna cikin wani mawuyacin hali, na kunchin rayuwa, “Munshirya wan nan tallafin ne don mu rage matsalar rashin aikin yi a Jihar Bauchi da kuma samar da aiyyukan yi na dogaro da kai a cikin al’umma.
Har’ Ila yau, yace duk abun da gwamnatin mu take yi ana tambanyan mutane ne irin kayan da suke su ma tallafi ko kuma zunzurutun kudi a dunkule domin ci gaba da sana’a ko kasuwan cin su, yace kowa abinda ya zaba shi za’abashi na kayan tallafin”.ya fada.
Kakakin majalisar Jihar Abubak Y Sulaiman a lokacin da yake tsokaci kan ayyukan tallafin yace hadin Kai shike kawu cin nasarar a abunda gwamnatin tasa a gaba domin al’umarta shiyasa a cewarsa mutanen Bauchi suke cin gajiyar romon democradiyya, yace “mu a majalisa kanmu a hade yake babu wata baraka, dukbda wadansu basu son hakan” yace Jihar Bauchi ce a gabansu.
Ana ta jawabin Uwargidan Gwamnan Jihar Aisha Bala Mohammed taja hankalin matasa a yankin da su guji tada fitina tare da bama yaya mata kariya ta wajen kawarda matsalar fyade a fadin jihar.
Kana tayi kira ga wadanda suka chi gajiyar kayan da suyi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace ba su kashe ba kuma su rungumi hannu, tace karsu yarda wan nan dama na tallafin ya wuce su.
Sanan tayi nuni da muhimmanci zamanl afiya a cewarta “shine ginshikin komai a a rayuwarmu in babu zaman lafiya yanzu da bamu samu sukunin zuwa wan nan taron ba., Kana ta roki wadanda basu samu tallafin ba, da cewa suyi hakuri wani lokaci zasu samu”.
Kwamishiniyar ayyukan hadin gwiwa da kananan masana’antu na Jihar Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi, tace a ma’aikatar ta tuni shiri yayi nisa na baiwa kana nan yan’kasuwa ranchen jarin kudi don habbaka kasuwanci da masu karamin karfi a masana’antu don ci gaban al’umman Jihar.
Haka nan a wajen taron ta bayyana irin kayan da gwamnati ta raba, wanda suka hada da Keken dinki, Injin matsan man gyada, Baburan hawa, Motocin hawa, kudade a dunkule da dai sauransu.
