Kungiyar zauren mutanen jihar Bauchi sun yi kira da a tabbatar da mulkin karba karba don yin adalci ma sauran sassan jihar tare da cigaba mai dorewa a dukkanin fadin jihar baki daya.
Sunyi wan nan kira ne a wajen wane taro na musamman da kungiyar ta shirya a karamar hukumar Ningi a ranar Asabar don tabbatar da adalci ga yayan jihar.
Shugaban kungiyar Alhaji Mohammed Danladi mai’auduga yace wan nan taro yana da matukar muhimmaci, san nan yaja hankalin mambobin kungiyar da su rika yin gaskiya da adalci da kuma kwarewa wajen aiwatar da aikin jama’a tukuru.
Daya daga cikin Iyayen kungiyar kuwa Abubakar Belly Tafawa Balewa, yace dole ne indai jihar Bauchi tana son ci gaba da adalci mai inganci dole abama kowani bangare dama domin tabbatar da adalci irin na mulkin siyasa.
Abubakar Billy, ya kara da cewa, “munyi shekaru fiye da 20 a siyasa, amma mu yan Bauchi ta kudu muke tayi, wan nan abu ya jawu mana ci baya a jihar Bauchi, kuma ba yan Bauchi ya kudu ce kawai tafi iya mulki ba, shekaru ashirin da aka yi baifi shekaru hudu ba na Tatari Ali ba”.
Salisu Ahmed Barau tsohon kwamishinan harkokin addinin musulunci na jihar, a wajen taron yace yankin arewaci da tsakiya saidai ai ta basu mataimaka ko kakakin majalisa, in gwamna baya nan sune da rike jijar yace irin wadan nan abubuwa ne zauren take so akawo sauyi domin kowa yasha rumun democradiyya basai yan bangare daya ba.
Ya kamata musan cewa gari ya waye, duk wani mai hazaka wanda bazai nuna banbanci ba, ya fito mu mara masa baya shekara biyo kenan duk abubuwan da akace za ayi ba ayisu ba” ya fada.
Shima Alhaji Ibrahim dogarai Ningi mai sharhi kan siyasar Najeriya da ma ta jihar Bauchin har ila yau, yace “ya kamata sauran yankin a zauna aga wadanda suka chanchanta, na farko ba wai mutumin da baya tsinanawa mutane komai ba, a duba wanda ke kyuatatawa sauran shiyyar ba irin wan nan gwamnatin ba ta yanzu a jihar Bauchi”
Daga karshe yace yayan jamiyyar APC ce ta kawo wan nan gwamnatin ba yan jamiyyar PDP ba. yace dole sai an sake karatun ta nutsu tu kunna kafin a iya samun chanji fa kowa zai na am dashi a jihar Bauchi.
a jihar Bauchi baki daya domin ciyar da jihar baki daya
Daga Adamu Shehu Bauchi
