Bauchi: An Horar Da Masu Sa Ido Akan Cin Zarafin Mata

A ci gaba da neman mafita kan cin zarafin yaya mata da yara kanana da ya addabi Jihar Bauchi, dama Nijeriya baki daya,wata kungiyar lauyoyi mata na kasa reshen Jihar Bauchi (FIDA) ta horar da wadanda zasu rika sa idanu sosai don zakulo masu aikata wan nan ta asa a cikin al’umma, domin su fuskanci hukunci mai tsanani.

Tun a farko, shugaban kungiyar Barrista Fatma Abubakar tace horarwan na kwana biyu ne, tare da sanin makaman aiki kan abunda zasu rika yi tace yana da muhimmanci, kuma zakulo muta nen ne daga kana nan hukumomi hudu na Jihar Bauchin

Tace makasudin taron, ya ta allaka ne kan irin gudumuwar da zasu bayar da kuma sanin hukunce hukunce na dokan kasa wanda ya aikata cin zarafin mata da yara da kuma sauran nau’oin cin zarafin dan adam a cikin al’umma, da sauran yankunan da aka turasu don gudanar da aikinsu ba tare da wata matsala ba.

Ta kara da cewa wan nan sanin makama zai kara masu himma da hazaka ta wajen samar da ci gaba a hidimar cin zarafin dan adam ta kowani fanni bisa ganin muhimmancin al’amarin da ya shafi cin zarafin mata da yaran.

Bugu da kari, Fatima Abubakar ta kara da cewa abun takaici ne ta yadda wadanda akaci zarafinsu ko suka samu kansu a cikin wannan mawuyacin hali na cin zarafi daga daidaikun mutane a cikin al’umma, tace basu iya magana saboda tsoron shiga matsalolin tsangwama a cikin jama’a.

Shugaban tayi kira ga al’umma dasu rika bada bayani akan alamari irin wan nan don a gudu tare a tsira tare, tace idan ana hukunta masu aikata fyade ko cin zarafin yaya mata ko wani abu maka mancin haka zasu rika shiga taitayinsu.

Ta jaddada cewa mutane su rika bude baki suna tona asirinsu ko da kowa yan uwan a cikin gida ko a waje inda tace abun yafi bada wahala in ya hada da zumunci tsakanin wanda aka keta mashi zarafi.

Ta kara da cewa hakan yana basu wahala matuka, amma don samun daman kaisu kotu don yanke masu hukuncin da doka ta tanada ma masu cin zarafin dan adam.

Daga karshe ta kara da hankalin wadanda suka sami horar war dasu wayar ma da mutane kai sosai don fahimtar inda akasa gaba kan wan nan mummunan dabi’a, a cikin al’umma.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment