Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ofishin dake kula da bashi a Najeriya ya ce bashin da ke wuyan gwamnati ya karu sosai a 2021.
Darakta-Janar ta Ofishin Patience Oniha ta bayyana hakan ta na mai cewa kudin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira Tiriliyan 32 a 2020 zuwa Tiriliyan 38 a 2021.
Patience Oniha tayi wannan bayani lokacin da ta zanta da manema labarai a Abuja, ta ce wannan ya kunshi bashin gwamnatin tarayya da na jihohi.
An yi amfani da wannan bashi wajen cike gibin da aka samu a kasafin kudi tare da yin ayyukan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.
Shugabar ta ?ara da cewar a shekarar bara, an ci bashi ne daga tsarin Eurobonds da Sukuk da sauransu. An yi amfani da kudin domin yi wa jama’a ayyuka.
“Gwamnatin tarayya ta lura da nauyin bashi ga kudin shigan gwamnati, kuma ta fara daukar matakan kara samun haraji da aka sa a dokar kudi tun 2019.”
