Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankunan ?asar za su ci gaba da kar?ar tsoffin takardun ku?i daga hannun kwastomominsu har zuwa bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu, lokacin da za a daina amfani da tsoffin takardun ku?in a ?asar
Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da ya hallara a gaban kwamitin wucin-gadi kan sauya fasalin ku?in ?asar na majalisar wakilan ?asar.
To sai dai gwamnan Babban Bankin bai bayyana lokacin da bankunan za su daina kar?ar tsoffin takardun ku?in ba.
Tun da farko dai kakakin Majalisar Wakilan ?asar Femi Gbajabiamila, ya zargi gwamnan Babban Bankin da sa?a wa sashe na 20 na dokar CBN wadda a cewarsa ta wajabta wa bankunan ci gaba da kar?ar tsoffin kudin har zuwa bayan wa’adin da Babban Bankin ya saka.
Yayin da yake jawabi a gaban kwamitin Emefiele, ya ce ya yarda da ‘yan majalisar game da sashe na 20 na dokar CBN.
”Sashe na 20 na cewa bayan cikar wa’adi za a daina amfani da tsoffin takardun ku?i, to amma an wajabta wa bankuna kar?ar ?u?a?en. Dan haka ina tare da majalisa a kan haka”, in ji Emefiele.
