Bada?akar Filaye: Masarautar Kano Ta Bijirewa Umarnin Kotu

Kwanaki ka?an bayan da wata Babbar Kotu a jihar Kano ta ba da umarnin hana Masarautar Kano yanka filaye a Filin Sallar Idi na ‘Yar Akwa, majalisar masarautar ta yi biris da umarnin Kotun inda ta ci gaba da yanka filayen.

Da yake jawabi ga manema labarai a farfajiyar filin ranar Asabar, shugaban kwamitin filin daga yankin, Tijjani Yahaya, ya ce sun yi mamakin cewa bayan umarnin kotu, sai kawai suka wayi gari da safe suka ga ana aikin yankan filin.

Ya bayyana cewa, ’yan sanda dauke da makamai a cikin motoci kusan biyar suna bai wa wasu mutanen da aka turo don yankan filin kariya.

Ya tunatar cewa filin da ake magana akai marigayi Sarki Ado Bayero ne ya bayar da shi ga mazauna yankin don amfani da shi a matsayin wurin Sallar Idi, wanda daga baya gwamnatin jihar Kano ta sanya shi a filyenta, bayan kirkirar Darmanawa Layout.

A cewarsa, a shekarar 2019, kungiyar ta nemi Ofishin kula da filaye ya shigo cikin lamarin lokacin da suka lura da yunkurin mamaye filin da Masarautar Kano ke kokarin yi, wanda shi ne kadai filin Idi a duk karamar hukumar Tarauni.

Bayan haka, shugaban ya bayyana cewa kungiyar ta tuntubi mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero game da yunkurin kwace filin da Ado Bayero Royal City Trust Fund ta yi don sauya filin zuwa wuraren zama tare da sayar dashi.

Ya kuma bayyana cewa Sarkin ya nemi bangarorin biyu da su tabbatar da zaman lafiya sannan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Malam Yahaya ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta yi duk abin da doka ta tanada don karewa da hana cin zarafi ba bisa ka’ida ba da kuma dakile yunkurin sayar da filin na Sallar Idi.

Mai magana da yawun Masarautar Kano Ahmad Bayero, bai amsa kira ba da sakon tes da aka nemi masarautar ta amsa kan lamarin.

Related posts

Leave a Comment