Babu Wata Barazana Game Da Zaben 2023 Dake Tafe – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa ‘yan ?asar cewa za a gudanar da babban za?en ?asar da ke tafe kamar yadda aka tsara.

Ministan ya?a labaran ?asar Lai Mohammed na ya bayyana haka a Abuja babban birnin ?asar a lokacin gabatar da ci-gaban da ma’aikatarsa ta samu ?ar?ashin gwamnati mai ci.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da kalaman da wani babban jami’i a hukumar za?en ?asar ya yi na cewa za?en ?asar na fuskantar barazanar sokewa saboda matsalar tsaro.

Ministan ya ce matsayar gwamnati ita ce za?en 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.

Ya ?ara da cewa ”babu abin da ya faru da ya sauya wannan matsayi. Mun sani cewa INEC na aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da samun nasarar gudanar da za?en a fa?in ?asar”.

“Hukumomin tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an gudanar da za?ukan cikin kwanciyar hankali. Dan haka babau wata fargaba”, in ji ministan

Hukumar Za?en ?asar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da za?en shugaban ?asa a ?asar.

Related posts

Leave a Comment