Babu Sulhu Tsakaninmu Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa – Gwamnatin Tarayya

IMG 20240225 WA0030

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa shugaban ?asa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya zama dole a ri?a ?aukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin ?an ta’adda.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron bu?e-baki tare da ma’aikatan shari’a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin al?alin al?alai na ?asa, mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Da yake nanata ?udirin gwamnati na mur?ushe ?an bindiga, shugaba Tinubu ya ce wa?anda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.

“Dole ne mu ayyana masu garkuwa a matsayin ?an ta’adda,” in ji shugaban ?asar, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ta ruwaito.

Najeriya dai tana fama da ?aruwar matsalolin tsaro. Yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas sun yi fama da ?aruwar sace-sacen mutane da hare-haren ?an bindiga a shekaru 10 da suka gabata.

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa ba za ta tattauna da ?an bindiga ba duk da yadda suka mayar da sace mutane don ku?in fansa a matsayin wata hanyar samun ku?i inda suke garkuwa da ?alibai da jama’a – hari na baya-bayan nan shi ne sace ?alibai 137 daga Kuriga a jihar Kaduna.

Related posts

Leave a Comment