Babu Hannuna A Rikicin Atiku Da Gwamnonin PDP – Jonathan

Tsohon Shugaban ?asa Goodluck Ebele Jonathan ya musanta zargin da ake yi cewa akwai hannunsa a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP mai adawa a ?asar.

Gwamnonin jihohi biyar ne a yanzu ke takun-sa?a da ?an takarar shugaban ?asa na PDP, Atiku Abubakar, kuma suka ha?i?ance cewa sai shugabanta na ?asa Iyorchia Ayu ya sauka daga mu?aminsa.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin ya?a labarai, Ikechukwu Eze ya fitar, Jonathan ya musanta zargin da ake yi cewa da sa hannunsa a rikicin.

“Mun samu labari maras tushe da ake ya?awa cewa gwamnonin da ke rikici da jam’iyya sun bayyana goyon bayansu ga Dr Goodluck Jonathan,” a cewar sanarwar. “Da mun ga dama za mu iya yin shuru da bakinmu saboda abin ba shi da wani tushe.

“Sai dai muna yin wannan bayani ne saboda ‘yan Najeriya da yawa sun nemi bahasi daga gare mu tare da nuna damuwa cewa za a iya kwarmata batun a jaridun ?asa.”

Gwamnonin da ake yi wa la?abi da G5 masu rigima da ?angaren Atiku su ne: Nyesom Wike na Ribas, da Seyi Makinde na Oyo, da Okezie Ikpeazu na Abiya, da Samuel Ortom na Binuwai, da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

A wani labarin na daban Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai tare da sauran gwamnoni uku masu adawa da takarar shugaban ?asa da Atiku Abubakar ke yi, sun kai wa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ziyara a ranar Laraba.

Ortom ya samu rakiyar Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Daga cikin hasalallun gwamnonin biyar, Gwamna Seyi Makinde na Oyo ne bai samu damar kai wa Gwamna Bala ziyarar ba.

Ortom wanda kuma shi ne Shugaban ?ungiyar Gwamnonin PDP Masu Muradin Gaskiya, ‘yan G5, sun yi ganawar sirri da Bala a cikin Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.

Wike ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, inda ya fara da bayar da ha?urin rashin zuwan Gwamna Makinde na Oyo, saboda ba ya ?asar.

Ya ce sun je ne domin su jajanta masa kuma su goya masa baya a kan sa?anin sa da Atiku Abubakar.

“Mun zo Bauchi domin mu ji abin da ya faru da shi, kuma idan akwai hanyoyin da za mu iya ba shi shawarwari nagari.

“Duk abin da ya shafi Gwamna Bala, to mu ma ya shafe mu. Dalilin zuwan mu kenan ba wani abu ba,” inji shi.

Da ya ke magana, Gwamna Bala ya ce ya yi farin cikin kar?ar ba?uncin gwamnonin wa?anda su ka je domin nuna masa goyon baya. Ya ?ara da cewa Bauchi ai gidan su ne.

“Su na kiran kan su PDP G5, ai ya kamata a ce ina cikin su, amma sai su ka maida ni saniyar-ware saboda wani dalili na su.

“Amma duk da haka babu ranar da ba zan yi waya da ?aya daga cikin su ba. Saboda ai wanda ra’ayin ku ya zo ?aya ai shi ne abin tuntu?ar ka kuma abin shawarar ka a kullum.

“Abin da ya fi burge ni game da su shi ne su na da ?arfin jure dafin kibiyar duk wani ?alubale.

“Ra’ayi na ya ?an sha bamban da na su, amma dai ina jin zafin abin da aka yi masu, su ma su na jin ciwon abin da aka yi min.

“Mu na fuskantar ?alubale a Bauchi, musamman na masu yin ‘anti-party’, masu shirya tuggu da ‘yan kitsa sharri,” inji Bala.

Bala ya ce ziyarar da gwamnonin su ka yi masa ta ba shi damar sanar da su damuwar sa, fargabar sa da kuma gagarumin hadarin da zai iya tirni?e su nan gaba.

Related posts

Leave a Comment