Babbar Magana: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun bu?e wa jerin gwanon tawagar motocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wuta akan hanyar Daura a ranar Talata.

A cewar mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ba ya cikin tawagar lokacin da aka kai harin.

Rahotanni sun bayyana cewar Jami’an tsaro da sauran yan tawagar shugaban ?asan na kan hanyar zuwa Daura, mahaifar Buhari yayin da bikin Babbar Sallah ke ?aratowa, lokacin da ‘yan bindigan suka farmake su a kusa da Dutsin-ma.

Related posts

Leave a Comment