An bayyana cewa babban gata da iyaye za su yi wa ‘ya’yan su shine basu ingantaccen ilimi na addini da na zamani wanda hakan zai sa su zama abin alfahari ga ?asa nan gaba.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a yayin bikin yaye daliban makarantar Nurul Huda da ya gudana a Arewa House Kaduna, Ambasada Dr Ismail Musawa ya ce ilimi bai da tsada ko da nawa za a kashe wajen neman shi.
Dr Musawa ya ?ara da cewa ilimi shi ne tsani guda da ya rage wanda ke kawar da dukkanin wata matsala ko fitina a tsakanin jama’a.
Ya kuma yaba shugabannin makarantar ta Nurul Huda inda ya bayyana su a matsayin jajirtattu wa?anda suka tsaya wajen bayar da ilimi yadda ya kamata inda ya kalubalanci sauran makarantu da suyi koyi da su.
